Nigeria: Ƙkaunar Buhari na neman hada faɗa

A Najeriya, yayin da aka ga kamun ludayin
gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, an fara
samun saɓanin ra'ayi tsakanin magoya bayansa
sakamakon matakin da wasu daga ciki ke ɗauka
na sukar wasu manufofin gwamnatinsa.
`Yan ga-ni-kashe-nin shugaban kasar dai na cewa
shugaba Buhari ba ya laifi, don haka bai kamata
a kushe masa ba, inda sukan maida raddi da
kakkausar kalamai idan ana muhawara da su kai-
tsaye ko ta shafukan sada-zumunta na zamani,
lamarin da ke rage tagomashin shugaban kasar a
zukatan masu sassaucin ra`ayi.
Duk da cewa duka ƙaunar mutum guda ce ta
haɗa su, masu sassaucin ra`ayi na ganin cewa
ba daidai ba ne su yi shiru a duk inda suka ga
shugaban kasar ya yi kuskure, saboda a ra`ayin
irin waɗannan mutane, mutum tara yake bai cika
goma ba, don haka kamar sauran jama'a,
shugaban kasar bai fi ƙarfin yin kuskure ba, kuma
yi masa gyara ko tsokaci wata siga ce ta ƙauna.
Sai dai ɓangaren shugaban kasar ya ce
demokradiyya ta gaji yabo da suka, don haka
babu dalilin fada da juna.
Masana dai na ganin cewa magoya bayan
shugaba Buhari na bukatar sake-lale a
muhawararsu, saboda masu sassaucin ra`ayi na
cewa azalzalar da `yan ga-ni-kashe-ni ke musu ta
sa ƙaunar da suke yi wa shugaban kasar ta fara
gushewa a hankali.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Ƙkaunar Buhari na neman hada faɗa"

Post a Comment