An kashe 'mutum 11' a tarzomar da ta barke a Kamaru

Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Bamenda
na Kamaru bayan da mutum 11 suka mutu a
tarztarzomar da ta barke tsakanin matasa da
jami'an tsaro a Arewa maso Yammacin kasar.
Wadanda suka shaida lamarin, wanda ya faru a
ranar Alhamis da yamma, sun ce jami'an tsaro
sun yi amfani da harsashe masu kisa wajen
tarwatsa zanga-zangar da a cewarsu, ta lumana
ce.
Mazauna birnin Bamenda sun yi ta watsa
hotunan tarzomar a shafin zumunta na
Whatsapp.
Wani Lauya a birnin ya shaida wa BBC cewa, ba
zai iya komawa gida daga wurin aiki ba, saboda
jami'an tsaro na amfani da harsashen gaske
wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Harmony Bobga, daga kungiyar lauyoyin Kamaru,
na daya daga cikin lauyoyin da ke jagorantar
fafutukar da ake yi na yaki da dokar da aka kafe
ta cewa dole a yi amfani da harshen Faransanci
a yankunan da ake yin Turanci a kasar.
Ya ce ya yi magana da wasu da lamarin ya afku
a gabansu, a wani babban asibiti da ke birnin,
inda suka shaida masa cewa fararen hula shida
da wani dan jami'iyya daya da kuma 'yan sanda
hudu sun mutu.
Tarzomar ta barke a yayin da jam'iyya mai mulki
ta soma gudanar da wani taron siyasa a
Bamenda.
Mista Bobga ya ce sun samu rahotanni cewa
Firayi Ministan Kamaru, Philemon Yang, wanda
shi ya kamata ya jagoranci taron siyasar, ya
boye a wani otal mai suna Abaya, a inda jami'an
tsaro suka tsaurar tsaro.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kashe 'mutum 11' a tarzomar da ta barke a Kamaru"

Post a Comment