Boko Haram: Jam'iyyar PDP ta yaba wa Shugaba Buhari

Babbar jam'iyyar hamayya ta Nigeria PDP ta yaba wa shugaban kasar Muhammadu Buhari bisa nasarar kakkabe 'yan Boko-Haram daga dajin Sambisa.
PDP ta ce ta jinjina wa Buhari bisa tsayuwar-dakan da ya yi a yakin da ake yi da 'yan Boko Haram.
Haka kuma jam'iyyar ta nuna farin ciki kan abin da ta ce ci-gaba da Buhari ya yi a kan kokarin da gwamnatin Goodluck Jonathan na PDP ta yi a yakin da ta'addanci.
Wata sanarwar da sakataren watsa labaran jam'iyyar Price Dayo Adoyeye ya fitar ta ce nasarar da aka samu a yakin da ake yi da Boko Haram ta samo tushe ne daga irin kokarin da gwamnatin baya ta yi, musamman 'yan makwanni, gabanin gudanar da zaben shuugaban kasa a shekarar 2015.
Sanarwar ta PDP ta kuma jinjina wa sojojin Nigeria bisa jajircewa a yukurin raba kasar da masu tada kayar baya.
To sai dai PDP ta ce kwace dajin Sambisa ba ya nufin cewa an kammala yaki da ta'addanci, ta yi kira hukumomin Nigeria su matsa-kaimi wajen kakkabe 'yan ta'adda daga dazukan kasar da dama da suka zama wata mafaka ga 'yan ta'adda.
Ba kasafai dai PDP ke yabawa Buhari ba, kuma a lokuta da dama tana caccakarsa kan koma baya a bangaren tattalin arziki.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Boko Haram: Jam'iyyar PDP ta yaba wa Shugaba Buhari"

Post a Comment