Buhari ya mayar wa Sarki Sanusi martani kan tattalin arziki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba
daidai ba ne kalaman da mai martaba sarkin
Kano Muhammadu Sanusi II ya yi cewa
gwamnatinsa ta karbi N4.5tr, yana mai cewa
N1.5tr ta karba.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar
Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, "Ina matukar
mutunta mai martaba saboda shi sarkina ne;
domin ni dan Kano ne. Amma akwai gyara a
alkaluman da ya bayar.
Gaskiya ne gwamnati ta karbi kudi sosai daga
babban bankin Najeriya, amma ba ta zarta ka'ida
ba."
Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi ya ce kudin da
gwamnati ta karba daga babban bankin Najeriya
sun ninka sau fiye da goma kan adadin da doka
ta ba su umarni.
Sai dai Malam Garba Shehu ya kara da cewa,
"Mu dauka maganar da ya fada gaskiya ce. Duk
da haka gwamnati tana da kudin da ya zarta
wanda ta karba a ajiye a asusun bai-daya. Kamar
mutum ne mai asusun banki biyu; daya babu
kudi, dayan akwai makudan kudi. Menene illar
kwaso kudin daya asusun domin biyan bukatar
al'umma?."
Kakakin na shugaban Najeriya ya ce ba zai yi wa
Sarki Sanusi raddi kan adawar da yake yi ga
kudirin gwamnati na karbi bashin $30bn, yana
mai cewa ministar kudi za ta tanka masa.
A cewarsa, "A matsayi na na dan kasa zan so na
sake karanta jawabinsa game da wannan batu.
Amma ai za a karbo bashin ne domin yin
ayyukan ci gaban kasar, cikinsu har da kafa
layukan jirgin kasa da samar da hasken wutar
lantarki."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya mayar wa Sarki Sanusi martani kan tattalin arziki"

Post a Comment