Shugaban Philippines ya tabbatar da cewar ya aikata kisan kai da hannunsa

Shugaban Philippines, Rodrigo Duterte, ya tabbatar da cewar ya kashe mutanen da ake zargi da aikata laifi a lokacin da yake magajin garin Davao.
Wannan ne karon farko da Duterte ya fadi hakan tun lokacin da ya zama shugaban kasar a watan Yuni, bayan wani ikirarin da ya taba yi a shekarar 2015.
Shugaban ya jagoranci Davoa shekara 20, inda ya yi fice wajen rage aikata laifuka tare da shan suka wajen goyon bayan hukuncin kisa.
Wadannan sune kalamai na baya-baya a jerin takaddama ko ce-ce-ku-ce da Duterte ke janyo wa.
Shugaban ya ce "A Davoa ina kisa da hannu na. Domin in nuna wa jami'an tsaro cewar, idan ni da kai na zan yi, to mai zai hana su".
"kuma ina zagayawa birnin Davoa a kan babban babur domin yin sintiri ko zanda ana hatsaniya, ina neman wanda zai tunkare ni saboda na kashe shi".
Shugaban ya tabbatar da kashe mutane uku a shekarar 2015 wadanda ake zargi da sace mutane da fyade a birnin.
Hukumar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi tur da kalaman na sa, inda ta bukaci da ya kawo karshen kashe mutane nan take.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shugaban Philippines ya tabbatar da cewar ya aikata kisan kai da hannunsa"

Post a Comment