Sanatoci sun yi watsi da naɗin Ibrahim Magu


'Yan majalisar dattawan Najeriya sun ki amincewa su tabbatar da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin kasa ta'annati.
'Yan majalisar sun ce sun dauki matakin ne bayan wani rahoto ya nuna cewa shugaban na EFCC na da hannun a taken hakkin dan adam.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa da safiyar Alhamis ne 'yan majalisar suka gayyaci Mr Magu zauren majalisar inda suka yi ganawar sirri da shi, kuma a lokacin ganawar ne suka shaida masa cewa hukumar tsaron kasar ta mika musu wani rahoto da ke zarginsa da hannu wajen take hakkin dan adam.
A cewar majiyar, bayan haka ne shugaban riko na EFCC din ya yi musu bayani kan rahoton, amma ba su gamsu da bayanansa ba.
Daga bisani ne suka yi watsi da tabbatar da nadinsa a matsayin shugaban dindindin na hukumar.
Da ma dai an dade ana kai ruwa rana game da batun tabbatarwa da Mr Magu mukamin nasa, inda wasu ke zargin 'yan majalisar na jan kafa kan batun saboda shari'ar da ake yi wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki bisa zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa, zargin da ya sha musantawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sanatoci sun yi watsi da naɗin Ibrahim Magu"

Post a Comment