Nigeria ta haramta shigo da motoci ta iyakokinta

Gwamnatin Nigeria ta haramta shigar da motoci
cikin kasar ta kan iyakokinta na kasa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar
hana fasakauri ta kasar ta fitar inda ta ce dokar
ba za ta fara aiki ba sai ranar daya ga watan
Janairu mai zuwa.
Hukumar ta ce haramcin ya shafi shigowa da
sababbi da kuma tsofaffin motoci, sai dai bai
shafi shigar da motoci zuwa kasar ta ruwa ba.
Wannnan mataki na haramcin shigar da motocin
ya zo ne bayan da gwamnatin ta haramta shigar
da shinkafa ta bakin iyakokin kasar tun daga
watan Afrilun 2016.
Hukumar hana fasakaurin ta kuma shawarci
maso shigowa da motoci ta kasa da su gaggauta
kwashe motocin da suka shigo dasu a ruwa
amma kuma suke wasu tashoshin jiragen ruwa
na wasu kasashe makwabta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria ta haramta shigo da motoci ta iyakokinta"

Post a Comment