Yanda Zaka Rage Wa Video Nauyi Ta Amfani Da Wayar Android

Jama'a barkanku da warhaka, Amanagurus ne ke muku lale marhabun da zuwa shafin mu mai albarka na arewamobile wanda ke kawo muku bayanai akan matsaloli da suka shafi wayoyin hannu da kuma bayanai kan manyan na'urori da sauran makamantan hakan.
A yau in sha Allahu zanyi bayani kan yadda zaku iya rage nauyin video ta hanyar amfani da wasu manhajoji na wayar hannu ta android wacce take mazaunin wayar da aka fi amfani da a wannan lokaci da muke ciki.
A bayyane yake cewar kowa na son ganin hoton video mai kyau (High defination) yayin da yake kallo musamman kallon fina-fina na cikin gida har ma zuwa na waje don jin dadin abinda mutum yake kalla. Sai dai kuma ba kowa bane burinsa ke cika akan hakan duba da irin yadda fina-finan ke zuwa da nauyi sakamakon ingancin da yake tattare da hotuna da kuma sautin muryoyin dake cikinsu(misali unconverted Mp4s).
Wasu lokutan kuma kila ka bukaci tura ma wani hoton video da aka dauka wajen bukukuwa ko kuma wasu tarurruka ta hanyar facebook, whatsapp ko kuma ta wata kafar sadarwar amma nauyinshi sai ya hana ka yin hakan duba da yanayin network mara karfi, ko rashin chaji isashshe ko kuma yanayin iyakar nauyin da kafar da zaka tura ta ita ta kayyade(upload limit).
Mutane da yawa sun sha tambayata kan ko akwai wasu apps da zasu iya amfani dasu wajen rage wa video nauyi don samun space da kuma samun damar kara wasu vidiyoyin akan wayoyinsu. Bisa wadannan dalilan dana zayyano yasa na yanke shawarar binciko gami da yin rubutu akan yadda mutum zai iya ragewa video nauyi.....
A can baya akan iya ragewa video nauyi ne kawai ta hanyar amfani da kwamfyuta, amma yanzu cigaban zamani ya kawo da yadda za'a iya yin amfani da wayar hannu wajen cimma aikin...
Abubuwan da ake bukata:
Ba wasu abubuwa ne masu yawa muke bukata ba, illa dai kawai muna bukatar wayar da za'ayi amfani da, sannan kuma sai daya daga cikin wadannan manhajojin(apps):
(i) Audio/Video Converter Android (Download it from playstore or simply click Here)
(ii) Video compressor (samo shi daga store ko kuma ka shiga nan
Da Audio/Video Converter Android zaka iya rage nauyin video din da yaka kamar 500mb zuwa 180mb ba tare da ingancin(quality) sa ya baci ba.
Haka zalika ma video compressor zai iya rage nauyi video da yakai 500mb zuwa 180 ko 200mb ba tare da rasa inganci ba, sai dai kuma Audio/Video converter android yafi video compressor sauri...
Ina fatan yanzu ba zaku kara yin kukan karancin guri ba yayin da kuke son dora video me nauyi zuwa wayoyinku na hannu.
Ina fatan zaku tura wa abokanenku wannan rubutu nawa ta hanyar sharin zuwa facebook, whatsapp, twitter da sauransu don suma su amfana.. Yi amfani da share buttons dake kasa...

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to " Yanda Zaka Rage Wa Video Nauyi Ta Amfani Da Wayar Android"

Post a Comment