Saudiyya ta yanke wa Iraniyawa hukuncin kisa saboda leken asiri

Wata kotu a kasar Saudiyya ta yanke wa
Iraniyawa 15 hukuncin kisa saboda kama su da
laifin leken asiri.
Mutanen na cikin mutum 30, yawancinsu 'yan
Shia na kasar Saudiyya, wadanda aka tsare
shekara uku da suka wuce sannan aka fara yi
musu shari'a a watan Fabrairu.
An kama su da laifin kafa wata kungiya da ke yi
wa Iran leken asiri da zummar yin kafar-ungulu
da kuma tayar da zaune tsaye a kasar ta
Saudiyya.
An yanke wa 15 daga cikin su hukunci dauri,
yayin da aka sallami mutum biyu saboda ba a
same su da laifi ba.
Kafofin watsa labaran Saudiyya sun ce akasarin
mutanen tsofaffin sojoji ne, wadanda ake zargi
da bai wa Iran bayanan sirrin Saudiyya.
Ana kallon wannan hukunci a matsayin wani batu
da zai kara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin
kasashen biyu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Saudiyya ta yanke wa Iraniyawa hukuncin kisa saboda leken asiri"

Post a Comment