Bounemouth ta doke Liverpool 4-3

Bournemouth ta doke Liverpool da ci 4 da 3 a
gidanta a karon farko a wasan gasar Premier na
mako na 14.
Sadio Mane ne ya fara ci wa bakin a minti na 20
da shiga fili, kuma minti biyu tsakani Origi ya
kara ta biyu.
A minti na 55 ne Bournemouth ta sako Ryan
Fraser sai wasa ya sauya salo, inda 'yan dakikoki
da shigarsa Milner ya doke shi alkalin wasa ya
bayar da fanareti, kuma Wilson ya buga ya ci.
Can ya kara ci wa Liverpool kwallonta ta uku a
minti na 64, amma kuma a minti na 76 Fraser ya
farke wa masu masaukin bakin ta biyu.
Bayan wasu mintina biyu ne kuma sai Cook ya
farke wa Bournemouth kwallo ta uku.
An shiga karin lokaci da minti uku, bayan minti
90 ne sai Ake ya ci wa Bournemouth kwallon ta
hudu, wadda ta ba ta nasara ta samu maki 18
kuma ta zama ta 14 a tebur.
Ita kuwa Liverpool yanzu ta zama ta uku a tebur
da maki 30, a bayan Arsenal mai maki 31, yayin
da Chelsea ke matsayin ta daya da maki 34.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Bounemouth ta doke Liverpool 4-3"

Post a Comment