An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa

An tsaurara matakan tsaro a manyan biranen
duniya yayin da ake shirin shiga sabuwar
shekara ta 2017.
A wasu biranen kasashen yamma, da suka hada
da London, da Brussels da Berlin, an girke karin
dubban 'yan sanda gabanin bukukuwan shiga
sabuwar shekarar.
An sanya shingaye na kankare a wuraren taruwar
jama'a a tsakiyar birnin Paris, da Madrid da New
York don kare aukuwar hare-hare da manyan
motoci, kwatan-kwacin wadanda aka kai a baya a
biranen Berlin da Nice.
An hana jama'a yin shagulgulan sabuwar
shekarar a Dhaka, babban birnin Bangladesh,
wanda ya yi fama da hare-haren 'yan bindiga
masu alakanta kansu da Musulunci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa"

Post a Comment