Masu kutse sun saci bayanan imel na mutum 1bn na Yahoo

Yahoo ya ce masu satar bayanai sun yi kutse a imel din mutum biliyan daya a shekarar 2013.
Kamfanin na intanet ya ce da alama wannan kutsen ya sha bamban da wanda aka yi a shekarar 2014 inda aka saci wasu bayanan imel din mutum 500m wanda ya bayyana a watan Satumbar da ya gabata.
Yahoo ya ce an sace bayanan da ke kunshe da sunayen mutane da wayoyinsu da bayanan sirrinsu da kuma adireshin imel dinsu, kodayake ba a saci bayanan asussan bankunansu da na biyan kudadensu ba.
Kamfanin, wanda kamfanin Verizon zai saye shi, ya ce yana yin aiki tare da 'yan sanda da hukumomi domin shawo kan wannan matsala.
Wata sanarwa da Yahoo ya fitar ta ce ya yi "amanna an yi kutse a cikinsa a watan Agustan 2013, sannan aka saci bayanan mutum sama da biliyan daya. Mai yiwuwa kutsen ya sha bamban da wanda a watan Satumbar 2016 muka ce an yi a baya."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Masu kutse sun saci bayanan imel na mutum 1bn na Yahoo"

Post a Comment