Mutum guda ya rasu a harin da aka kai kasuwar maiduguri

Jami'ai a Najeriya sun tabbatar da cewa wasu 'yan mata biyu sun kai tagwayen hare-hare a wata kasuwa da ke jihar borno, tare da hallaka mutum guda da jikkata wasu.
Wani ganau kan lamarin a birnin Maiduguri, ya ce su ma matan sun rasu a nan take, kuma dukka su biyun ba za su wuce tsakanin shekara bakwai zuwa takwas ba.
'Yan sanda a jihar borno, sun ce harin na kunar bakin wake ne da 'yan matan suka kai, a lokacin da ake tsaka da hada-hada a kasuwar da ke birnin Maiduguri.
Wani dan kato da gora ya shaidawa BBC cewa 'yan matan da suka kai sun zo ne a cikin babur mai kafa uku wato keke napep, ya kuma yi kokarin tsaida daya daga cikinsu, amma sai taki tsayawa tare da nufar taron wasu mutane da ke saida kaji, ba tare da bata lokaci ba ta tada bam din da ke jikinta.
A lokacin da mutane suka taru dan kaiwa wadanda suka jikkata dauki, ita ma dayar yarinyar sai ta tashi bam din da ke jikin ta.
Lamarin da ya sanya kasuwar ta yamutse aka fara gudun ceton rai.
Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, to amma a baya masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram da ke kaddamar da hare-haren su a arewa maso gabashin Nigeria musamman a jihar ta Borno, sun sha kai hare-hare a kasuwannin da ke cikin birnin da ma kauyuka har da jihohin Adamawa da Yobe masu makoftaka da jihar Borno.
Harwayau kungiyar na yawan amfani da 'yara mata kanana da 'yan mata har ma da tsofaffi wajen kai harin kunar bakin wake a jihohin arewa maso gabashin kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mutum guda ya rasu a harin da aka kai kasuwar maiduguri"

Post a Comment