Ɗan ga-ruwan da ke bai wa ma'aikatan gwamnati rance

Wani dan ga-ruwa, Abubakar Idris ya shaida wa BBC cewa kudin da yake samu ta hanyar sana'arsa sun ishe shi gudanar da harkokinsa har ma ya bayar da rance.
Abubakar, wanda ya ce a kullum yana samun daga N1000 zuwa N3000, ya ce ba zai iya yin aikin gwamnati ba musamman idan aka yi la'akari da cewa sai wata-wata ake daukar albashi.
Ya kara da cewa, "Ni mutumin jihar Kaduna ne da ke sayar da ruwa a nan Abuja; ina samun kudi daidai gwargwado, kuma kamar yadda na ga ma'aikatan gwamnati na korafi kan albashi, gaskiya ba zan iya yin aikin albashi ba."
"Sau da dama ma'aikatan gwamnatin da nake kai wa ruwa suna tambaya ta na ranta musu kudi kafin karshen wata; ka ga kuwa ai ba zan iya yin sana'a irin tasu ba," in ji Abubakar.
Ya yi kira ga matasa su tashi su nemi na kansu maimakon sai sun jira an ba su abin kashewa.
Abubakar ya ce, "Ya kamata matasa su sani cewa babu nakasasshe sai kasasshe. Da wannan sana'a nake ci, nake sha, nake biya wa iyalai da 'yan uwana nasu bukatun. Don haka babu abin da zan yi sai godiya ga Allah."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ɗan ga-ruwan da ke bai wa ma'aikatan gwamnati rance"

Post a Comment