Nigeria: Mata sun yi zanga-zanga tsirara, suka fasa motocin El-rufa'i

Wasu fusatattun mata sun yi zanga-zanga tsirara a yankin Kudancin Kaduna, kwana daya bayan wani rikici da aka yi a Kafanchan.
Mutane da dama aka kashe sakamakon rikicin da ya barke lokacin da matasan yankin suka yi wata zanga-zanga a ranar Litinin.
Matan sun yi zanga-zangar ne yayin da tawagar gwamnan jihar Malam Nasir El-rufa'i ta kai ziyara yankin, don ganin irin ta'adin da aka yi.
Fisatattun sun kuma farfasa motocin tawagar gwamnan sakamakon jefe-jefe da suka ringa yi da duwatsu.
Masu zanga-zangar dai sun fito ne duk kuwa da dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka ayyana, inda suka ce sun gaji da kashe-kashen mutane da ake yi a yankin.
Tun da farko dai, gwamnan jihar ta Kaduna ya yi wa matan jawabi, sannan ya kuma amsa tambayoyinsu.
Wakilin BBC da ke cikin tawagar ya ce zanga-zanagr matan tsirara ta kunyata duka mutanen da suka halarci wajen.
Gwamna El-rufa'i ya shaida wa matan an kara daukar matakan tsaro domin kawo karshen rikici a yankin.
Wakilinmu ya ce an yi ta'adi sosai yayin zanga-zangar da aka yi ranar Litinin wacce ta rikide zuwa kone-konen wurare, ciki har da masallatai da kuma coci-coci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Mata sun yi zanga-zanga tsirara, suka fasa motocin El-rufa'i"

Post a Comment