Abin al’ajabi: An haifi jaririya da kawuna 2 a Legas

- Wannan shine lokacin farko da zan ga irin wannan abu
- Wannan wani irin abu ne da ke faruwa wanda likitoci ke kira da Parapagus
Abin al’ajabi: An haifi jaririya da kawuna 2 a Legas
Abin al’ajabi: An haifi jaririya da kawuna 2 a Legas
Mutanen unguwan Ogudu a jihar Legas sun ga abin al’ajabi yayinda aka hafi wata jaririya da kawuna biyu.
Game da cewan rahotanni, jariryar mai kawuna biyu da iskar nishi na bature a kowani kai. Tana da wuya daya, kirji daya, kafafu da hannuwa 2. Wannan wani irin abu ne da ke faruwa likitoci sun ace masa Parapagus.
Likitocin asibitin Med-In Specialist Hospital, Osogbo Street,wadanda suka ciro jariryar sun bayyana cewa an Haifa jaririyar ne mislain karfe 6:30 na yamma a ranan Talata ta hanyar tiyata.
Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa a asibitin ranan Laraba, an tayar da jariryar kuma an kaita asibitin Jami’ar jihar Legas domin kula.
Game da cewan wata ma’aikaciyar sibitin da suka ciro ta, sun shiirya ciro yan biyu ne amma abin mamaki sai suka ansu a hada.
“Wannan shine lokacin farko da zan ga irin wannan abu. Na kasance ina kallo a Fi mamma ban taba gani a gaske ba . Amma,an gode likitan yace sun rayu.
“A yanzu da nike muku Magana, mahaifiyarsu bata san halin da suke ciki ba. Tana jiran ne kawai ta dauki yan biyun ta. Bamu fada mat aba tukunna. Mijinta ne kawai aka fada mawa kuma yana tare da likitocin yayinda aka kaisu asibitin Jami’ar Legas.”

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Abin al’ajabi: An haifi jaririya da kawuna 2 a Legas"

Post a Comment