China ta gargadi Donald Trump kan Taiwan

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce ta shigar
da korafi kan wayar tarhon da shugaban Amurka
mai jiran gado Donald Trump ya yi da shugabar
kasar Taiwan.
China na kallon Taiwan a wani bangare nata da
ya balle.
Dokokin Amurka sun sa kasar ta katse duk wata
hulda da Taiwan a hukumance tun a shekarar
1979.
Amma kwamitin karbar mulki na Mr Trump ya ce
Trump din da Shugaba Tsai Ing-wen sun bukaci
yin "hulda ta kut-da-kut da juna kan kasuwanci
da siyasa da kuma tsaro", lokacin wayar da suka
yi.
China ta ce ta mika "koke na musamman" ga
gwamnatin Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ambato
mahukuntan kasar China na bukatar Amurka da
"ta yi takatsantsan kan huldarta da Taiwan
domin gujewa abin da zai shafi dangantaka
tsakanin China da Amurka".
Tun da farko dai wasu rahotanni sun ce ministan
harkokin wajen China Wang Yi ya bayyana wayar
da shugabannin biyu suka yi a matsayin wata
"babbar yaudara daga bangaren Taiwan."
Trump ya taya Taiwan murna
Mr Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa
Ms Tsai ce ta kira wo shi domin ta yi masa
murnar lashe zaben Amurka.
Masu magana da yawunsa sun ce shi ma ya taya
ta murnar zama shugabar Taiwan a zaben da aka
yi a watan Janairu.
Wayar da Mr Trump ya yi kai-tsaye da shugabar
Taiwan abu ne da ba a saba ganin wani
shugaban Amurka ya yi ba.
China tana da daruruwan makamai masu linzami
jibge suna kallon Taiwan, kuma ta yi mata
barazanar yin amfani da karfin soja idan ta nemi
zama mai cin gashin kanta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "China ta gargadi Donald Trump kan Taiwan"

Post a Comment