Malaysia ta gargadi Myanmar kan kisan Musulmi

Ma'aikatar kasashen waje ta Malaysia ta fitar da
wata kakkausar sanarwa da ke fallasa irin kisan
kiyashin da makwabciyarta, Myanmar ke yi wa
tsirarun musulmai 'yan kabilar Rohingya.
Kasar ta Malaysia ta ja hankalin Myanmar da ta
taka wa wannan mummunar dabi'a birki bisa
la'akari da irin illar da take haifar wa ta fuskar
jinkai.
Sai dai kuma Myanmar din ta yi gargadin cewa
wahainiyar Malaysia ta kiyayi ramarta.
Amma Malaysia ta ce abin da ya sa take son yin
ruwa da tsaki a al'amarin, batun jinkai ne, ba wai
saboda addininsu daya da 'yan kabilar ta
Rohyngya ba.
A kwanan baya ma wani babban jami'ai na
majalisar dinkin duniya ya shaida wa BBC cewa
gwamnatin Myanmar tana yi wa Musulmi 'yan
kabilar Rohingya tsiraru kisan kare-dangi.
John McKissick na hukumar kula da 'yan gudun
hijira ta majalisar dinkin duniya ya ce dakarun
sojin kasar dai sun yi ta kisan 'yan kabilar ta
Rohingya a jihar Rakhine, lamarin da ya tilasta
musu tserewa zuwa makwabciyar kasar
Bangladesh.
Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da hare-haren
da ta ce na kawar da masu tayar da kayar baya
ne da ke kai hare-hare a kan iyakarta tun watan
Oktoba.
Ta musanta zargin da babban jami'n majalisar
dinkin duniyar ya yi.
Jami'an gwamnatin sun ce 'yan kabilar ta
Rohingya suna banka wuta kan gidajensu a jihar
ta Rakhine domin su dora alhakin hakan kan
gwamnati.
BBC ba za ta iya zuwa yankin domin tantance
gaskiyar al'amari ba saboda an hana 'yan jarida
da masu bayar da agaji shiga yankunan.
'Yan kasar ta Myanmar 'yan kabilar Buddha
mafiya rinjaye suna yi wa Musulmi 'yan kabilar
Rohingya, wadanda suka kai miliyan daya, kallo a
matsayin bakin-haure da suka shiga kasar daga
Bangladesh.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Malaysia ta gargadi Myanmar kan kisan Musulmi"

Post a Comment