Buhari ya bi a hankali wajen cin bashin $30b— Sanusi

Mai martaba sarkin Kano a Najeriya, Alhaji
Muhammadu Sanusi ya ce kuskure ne
gwamnatin kasar ta ce za ta ciwo bashin kusan
dala biliyan talatin, akan cewa za ta biya bashin
a cikin shekaru biyu.
Da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, Sarki
Sanusi ya ce ciwo bashin, abu ne mai kyau,
amma idan har gwamnatin za ta samu sassauci
a yarjejeniyar bashin, sannan kuma a yi amfani
da kudin wajen bunkasa bangaren makamashi, da
lantarki da gina hanyoyi.
Sai dai Sarkin ya ce ba ya tunanin abu ne mai
yiwuwa gwamnatin Najeriyar ta iya samo bashin
dala biliyan talatin din a cikin shekaru biyun da
suka rage mata, tun da har ta kasa samo dala
biliyan biyu a shekaru biyu.
Ya ce bisa alkaluman tattalin arzikin Najeriya na
yanzu, mawuyaci ne gwamnatin tarayya ta iya
samo bashin kudin da take so, ko da a ce
majalisar dokokin kasar ta amince mata hakan.
Alhaji Sanusi ya shawarci shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari da ya fi dora fifiko wajen
farfado da tattalin arzikin kasar.
Ya ce hakika gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli
daga gwamnatin da ta gabata, amma kuma ba ta
dauki matakan da suka dace ba na gyara kura-
kuran gwamnatin da ta gabata, da kuma farfado
da tattalin arzikin kasar.
A baya bai, shugaban Najeriya ya ce karbo
bashin dala biliyan talatin din ya na da
muhimmanci saboda karancin kayan bunkasa
tattalin arziki da kasar ke fama da su a dai-dai
lokacin da farashin man ya fadi a kasuwannin
duniya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya bi a hankali wajen cin bashin $30b— Sanusi"

Post a Comment