Wani dan bindiga ya kashe mutum 39 a Turkiyya

Wani mutum dauke da bindiga ya kashe mutum
39 sannan ya jikkata 40, a wani hari da ya kai
gidan rawa.
Harin wanda aka kai a birnin Istanbul na
Turkiyyar, ya janyo mutane da dama sun kuma
fada cikin kogi sakamakon gudun ceto rai.
Kididdiga dai ta nuna akwai mutum fiye da 700 a
gidan rawar lokacin da abin ya faku.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce mutumin ya
yi shigar burtu ne, har ya samu ya shiga gidan
rawar.
Daga nan kuma sai ya bude wuta a inda nan
take ya kashe mutanen.
Rahotannin dai sun tabbatar da cewa dan sanda
daya na daga cikin mamatan.
Daman dai akwai 'yan sandan ko-ta-kwana fiye
da dubu 16 a birnin na Istanbul saboda yawaitar
hare-haren ta'addanci.
Ko a makonni biyun da suka gabata ma sai da
aka harbe jakadan kasar Russia har lahira.
Sau shida ne dai hare-haren da ke haddasa
mutuwa da jikkatar mutane suka faru a 2016 a
kasar musamman a biranen Ankara da Istanbul.
Kuma fiye da mutane 200 sun mutu a hare-haren
guda shida.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wani dan bindiga ya kashe mutum 39 a Turkiyya"

Post a Comment