An sake kulla yarjejeniyar kwashe mutane daga Aleppo

Gwamnati da 'yan tawayen Syria sun ce sun kulla sabuwar yarjejeniya ranar Asabar da za ta bayar da dama a kwashe dubban mutanen da ba a fitar ba daga yankunan da ake fafatawa na kasar.
Dubban farar-hula da 'yan tawaye na sa ran ficewa daga Aleppo bayan dakarun gwamnati sun kame yankuna da dama na birnin.
A cikin yarjejeniyar, za a bar dubban mutane su fice daga garuruwan da ke hannun gwamnati da na 'yan tawaye.
An fitar da akalla mutum 6,000 daga Aleppo sai dai an dakatar da fitar da su ranar Juma'a.
An shiga rudani a ranar ta Juma'a sakamakon tsayar da fitar da mutanen da aka yi.
Gwamnati ta ce mayakan da ke goyon bayan 'yan tawaye sun rikka harbin ayarin mutanen da ke fita daga birnin.
Sai da 'yan tawayen sun ce dakarun gwamnati ne suka bude musu wuta.
Ana sa ran kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya zai kada kuri'a a karshen mako a kan daftarin da Faransa ta mika domin ganin kasashen duniya sun ja ragamar fitar da farar-hula daga birnin Aleppo.
'Yan jaridar da ke yankin sun ce mutane na matukar fama da yunwa.
Ranar Juma'a Shugaba Barack Obama na Amurka ya zargi Shugaba Bashar al-Assad na Syria da abokansa, wato Rasha da Iran da "cin zarafin farar-hul", yana mai cewa kawunan kasashen duniya sun hadu domin tunkarar matsalar Syria.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An sake kulla yarjejeniyar kwashe mutane daga Aleppo"

Post a Comment