MDD ta nemi Yahya Jammeh da ya rungumi kaddara

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah-wadai da shugaban Gambia, Yahya Jammeh bisa mayar da hannun agogo bayan da ya yi.
Kwaminitin ya kuma bukaci shugaba Jammeh da ya mika mulki ga Adama Barrow, a watan Janairu kamar yadda ya alkawarta tun da fari.
Zababben shugaban dai, Adama Barrow, ya ce, shi ba zai kira da ayi sabon zabe a kasar ba kamar yadda Yahya Jammeh ya bukata.
Ya kuma ce yana da yakinin cewa sojoji suna tare da shi a kan wannan batu.
Tuni dai Tarayyar Afirka ta bayyana kin amincewa da sakamakon zaben da shugaba Jammeh ya yi yanzu a matsayin abin da ba zai yiwuwa.
Ministan harkokin wajen Senegal ma ya gargadi shugaba Jammeh da kada ya yi yunkurin tauye wa jama'ar kasar 'yancin su.
Kasar ta Gambia dai ta shiga cikin wata dambarwar siyasa, bayan shugaban kasar Yahya Jammeh ya janyen sanarwar da ya bayar a makon jiya, cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar.
Shugaba Jammeh ya ce ya na so a sake gudanar da zaben, duk da kiraye-kiraye da Tarayyar Afirka ta yi na ganin ya mika mulki cikin kwanciyar hankali.
Adama Barrow dai ya dage kan cewa shi ne ya yi nasara a zaben, sannan ya bukaci jama'ar Gambia da su yi zanga-zanga.
Duk da wannan dambarwa dai, babu wata hatsaniya a cikin unguwanni a Banjul, babban birnin Gambia.
Akasarin mutane sun yanke shawarar zama a cikin gidajensu, saboda fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali.
An ga sojoji dauke da manyan bindigogi a muhimman wurare a babban birnin kasar.
'Yan kasar ta Gambia dai yanzu, sun zura ido domin ganin abin da zai faru.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "MDD ta nemi Yahya Jammeh da ya rungumi kaddara"

Post a Comment