EU ta ba wa Niger $ 600m kan 'yan cirani

Kungiyar Tarayyar Turai, wato EU, ta ba wa jamhuriyar Niger kudi fiye da Dala 600 domin dakile kwararar 'yan cirani da ke ratsawa ta kasar zuwa Turan.
Yankin Agadez mai yawan hamada dai ya zamo wata kafa ta bakin haure da ke bi domin ketarawa zuwa Libya kafin daga bisani su karkare a nahiyar Turai.
Tarayyar ta Turai dai ta ba wa kasashe irin su Senegal da Ethiopia da Najeriya da Mali irin wadannan kudade wajen hana bakin hauren kwarara.
Hakan ne ya sa aka samu raguwar hanyoyin da bakin hauren ke bi daga dubu 70 zuwa 2,000, a watan Nuwamban da ya gabata.
Hukumomi a Niger sun yi alwashin yakar al'amarin kan jiki-kan-karfi duk da cewa ba su ambaci kudin da Tarayyar Turan ta ba su ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

2 Responses to "EU ta ba wa Niger $ 600m kan 'yan cirani"