Jami'an tsaro sun mamaye hukumar zaben Gambia

Shugaban hukumar zabe ta Gambia ya ce jami'an tsaro sun kwace iko da babban ofishin hukumar, inda suka hana ma'aikata shiga.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da wasu shugabannin kasashen Afirta ta Yamma suka isa kasar domin shawo kan Shugaba Yahya Jammeh ya amsa kayen da ya sha a zaben.
Shugaban kungiyar ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.
Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya kayar da Mista Jammeh a zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya.
A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jami'an tsaro sun mamaye hukumar zaben Gambia"

Post a Comment