'Yan Majalisar Dattawan Nigeria shirme suke yi —Babachir

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Babachir Lawan ya yi watsi da kiran da 'yan majalisar dattawan kasar suka yi na a sauke shi daga kan mukaminsa sannan a hukunta shi.
Sanatocin sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki wannan mataki ne bayan binciken da suka gudanar ya nuna cewa Mr Lawan yana da hannun wajen kashe kudin da aka ware domin kula da 'yan gudun hijirar da Boko Haram ta fatattaka daga gidajensu ba bisa ka'ida ba.
Wani rahoto da 'yan majalisar suka fitar ya zargi Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a karbar kwangilar "cire ciyawa" a sansanin 'yan gudun hijirar, inda suka karbi makudan kudade ba tare da yin aikin da ya kamata ba.
Baya ga haka, 'yan majalisar sun yi zargin cewa Babachir Lawan ya sabawa ka'idojin aiki saboda ci gaba da zamansa shugaban kamfanin duk da cewa an nada shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
'Shirme suke yi'
Sai dai Babachir Lawan ya ce "Sanatocin shirme kawai suke yi; suna yunkuri ne kawai na ganin bayana. Suna so su rusa ni."
Ya kara da cewa,"Na ga rahoton da suka fitar, inda suka ce ban sauka daga mukamina na shugabancin kamfanin Rholavision Nigeria Limited. Amma ina son gaya muku cewa, na kafa kamfanin a watan Disambar 1990, kuma na sauka daga shugabancin kamfanin a watan Agustan 2015."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Majalisar Dattawan Nigeria shirme suke yi —Babachir"

Post a Comment