Buhari ya gabatar wa Majalisa kasafin kudin 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2017 ga 'yan majalisar dokokin kasar ranar Laraba.
Da yake jawabin mika kasafin kudin, Shugaba Buhari ya ce za a kashe N7.298tr a shekarar ta 2017, wato karin fiye da kashi 20 a kan kasafin kudin shekarar 2016.
Ya ce za a kashe kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin domin gudanar da manyan ayyuka.
Shugaba Buhari ya kara da cewa kasafin kudin zai bayar da muhimmanci wajen farfado da masaku a Aba da Onitcha da Kaduna da Kano da Nnewi da kuma Otta.
A cewarsa, za a yi amfani da kudin da ake samu ta hanyar man fetur wajen inganta harkar noma.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya ce zai kara N70 bn zuwa N100 bn fannin shari'a domin hana cin hancin da ake zarginsu da aikatawa.
Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne bayan da majalisar zartarwar kasar ta amince da gabatar da daftarin kasafin kudin a zaman da ta yi ranar 30 ga watan Nuwamba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya gabatar wa Majalisa kasafin kudin 2017"

Post a Comment