Babu shinkafar roba a Nigeria - NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna
ta Najeriya (NAFDAC) ta ce sakamakon gwajin
da aka yiwa shinkafar da jami'an hukumar
kwastam na kasar suka kwace ya nuna cewa
shinkafar gurbatacciya ce ba ta roba ba.
Wani babban jami'i a hukumar ya ce shinkafar
dai na dauke da kwayar cutar bakteriya ne wadda
ta wuce adadin da aka amince da ita.
Jami'an hukumar ta kwastam sun hakikance
cewa shinkafar da suka kwace a Lagos a makon
jiya ta roba ce, lamarin da ya haifar da cece-
kuce har ministan lafiya na kasar ya shiga
tsakani yana mai cewa ba bu wata shaida da ta
tabbatar da hakan.
Gwajin da aka yiwa shinkafar dai ya tabbatar da
cewa amfani da ita zai iya haifar da illa ga
al'umma saboda kwayar cutar bakteriyar da ke
cikin shinkafar ta wuce kima.
Hukumar kwastam ta ce ta kwace shinkafar ne
bisa bayanan da ta samu cewa za a shigo da
shinkafar roba mai yawa daga Asiya zuwa Afrika.
Duk da cewa sakamakon gwajin shinkafar ya
tabbatar da cewa gurbatacciya ce, har yanzu
wasu bayanai sun nuna cewa akwai tan-tan na
lalatacciyar shinkafa da aka ajiye a rumbunan
tara abinci da ke kasashe makwabta.
Shinkafa dai itace abinci na farko da 'yan
Najeriya suka fi amfani da ita, kuma itace akafi
bayarwa kyauta idan wani sha'ani ya tasowa
mutum.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Babu shinkafar roba a Nigeria - NAFDAC"

Post a Comment