'Zai wuya Zakzaky ya zauna a wani gari ba Zaria ba'

Kungiyar 'yan uwa Musulmai ko kuma Islamic
Movement of Nigeria bai bin tafarkin Shi'a, ta
ce, ta yi farin ciki da hukuncin da babbar kotun
Abuja ta yanke na a saki shugabanta, Sheikh
Ibrahim Zakzaky.
A ranar Juma'a ne dai alkalin wata babbar kotun
Najeriya, Mai shari'a Gabriel Kolawole, ya yanke
cewa gwamnati ta saki Elzakzaky cikin kwana
45.
Sannan kuma a ba shi diyya shi da mai dakinsa
ta Naira Miliyan 25 kowanennen su.
Kotun ta kuma umarci gwamnati da ta gina wa
shugaban na IMN gida a duk inda yake so
kasancewar an ruguje gidansa.
To sai dai wasu jiga-jigan 'ya'yan kungiyar sun
fara yin tsokaci dangane da batun sake gina
gidan a Zaria ko kuma a wani gari daban.
Malam Abdulhameed Bello wanda shi ne jagoran
'yanuwa musulmin a Zaria, ya ce, sun yi murna
da jin hakan amma fa ba ya tunanin El-zakzaky
zai so zama a wani gari sabanin mahaifarsa,
Zaria.
Tun dai watan Disamba Elzakzaky yake tsare a
hannun gwamnatin Najeriya, bayan wani farmaki
da sojojin kasar suka kai wa mabiyansa bisa
zargin yunkurin halaka babban hafsan sojin
kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Zai wuya Zakzaky ya zauna a wani gari ba Zaria ba'"

Post a Comment