MDD: Amina Mohammed ta zamo mataimakiyar Sakatare-Janar

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai jiran gado, Antonio Guterres, ya nada Ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.
Mista Guterres ya kuma nada wasu mata biyu a wasu manyan mukamai a majalisar.
Guterres ya mayar da hankali sosai wajen daidaita sahu tsakanin maza da mata, a wa'adinsa da zai fara daga ranar 1 ga watan Junairun 2017.
Babbar jami'a a ma'aikatar harkokin wajen Brazil, Maria Luiza Ribeiro Viotti ce za ta rike mukamin shugabar ma'aikata a ofishin sabon sakatare-janar din.
Ita kuma Kyung-wha daga Koriya Ta Kudu, an nada ta a matsayin mai bayar da shawara kan tsare-tsare.
Dama an yi ta rade-radin cewa za a nada Amina Mohammed a wannan mukami ganin irin nasarar da ta yi wurin jagorantar yarjejeniyar sabbin muradun karni na ci gaba mai dorewa da aka kulla.
Viotti kuma, wacce ita ce mataimakiyar sakataren Brazil a Asiya da yankin Pacific a yanzu, ta yi aiki a matsayin jakadar Brazil a Jamus, kuma ta wakilci Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "MDD: Amina Mohammed ta zamo mataimakiyar Sakatare-Janar"

Post a Comment