'Yan Shi'a za su kai gwamnatin Kaduna kotu

Kungiyar 'yan uwa Musulmi wato 'yan Shia da ke
Najeriya sun ce za su kai karar gwamnatin jihar
Kaduna saboda haramta ayyukanta da ta yi.
Kakakin kungiyar, Malam Ibrahim Musa, ya
shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatin jihar
ta Kaduna ta dauka bai yi musu adalci ba don
haka za su je kotu ne domin ta bi musu
hakkinsu.
Ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne
domin bata musu suna a idanun al'uma.
Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta amince da
wasu shawarwari na wani kwamitin bincike da ta
kafa bayan tashin hankalin da aka yi tsakanin
sojoji da mabiya kungiyar a birnin Zaria a watan
Disambar da ya wuce.
Tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar
daruruwan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi, a
cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta
Amnesty International.
Kazalika an kama shugaban kungiyar Sheikh
Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da 'yan kungiyar
da dama, kuma har yanzu ana ci gaba da tsare
shi duk da izinin da kotu ta bayar na sakinsa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Shi'a za su kai gwamnatin Kaduna kotu"

Post a Comment