Ba za mu yi rijista ba tun da ba kungiya ba ce — Shi'a

Harka islamiyya ko kuma Islamic Movement of Nigeria ta mabiya mazhabar Shi'a, ta ce ba za ta yi rijista ba, domin kira take yi, ba kungiya ba ce.
Wani jami'in tafiyar, Barista Haruna Magashi ne ya bayyana hakan a wani taron sasanta rikicin 'yan Shi'ah da 'yan sanda, a jihar Kano.
Tun da farko, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Toluse O. Emmanuel ya nanata cewa matukar mutum ko kungiya suka nemi izinin yin 'halartaccen' taro, ba shakka 'yan sanda za su ba su dama.
Barista Magashi ya koka a kan yadda mutane ke 'shayin' kusantarsu don jin abin da tafiyarsu ta kunsa daga bakinsu.
Wani mai gabatar da mukala a taron, Prince Ajayi Memaiyetan ya soki lamirin yadda 'yan sanda ke amfani da bindiga don tarwatsa jerin gwanon 'yan Shi'a.
Sai dai kuma wasu masu magana da dama a wurin taron, sun ce ba dai-dai ba ne yadda harka islamiyya ke gudanar da taro, ba tare da neman izinin hukuma ba.
Wannan dai wani matakin farko ne na tattaunawa kan rikicin 'yan Shi'a da jami'an tsaro kuma ya samu wakilcin mabiya addinai daban-daban.
Sharhi, Usman Minjibir
Tun dai watan Disambar 2015, lokacin da gwamnatin Najeriya ta kama shugaban Islamic Movement of Nigeria, Sheikh Ibahim El-zakzaky, mabiya malamin ke ta faman yin jerin gwano domin ganin an sake shi.
To sai dai jami'an tsaro musamman 'yan sanda na ganin jerin gwanon ya saba dokar kasa saboda rashin neman izni.
'Yan uwa musulmi dai na cewa koda sun nemi izni a wurin 'yan sanda ba za su ba su ba.
Babban al'amarin da ya faru tsakanin 'yan sanda da 'yan Shi'a, a baya-bayan nan, shi ne, lokacin da 'yan sanda suka tarwatsa wani tattaki da 'yan Shi'ar suka so yi daga birnin Kano zuwa Zaria.
Mutane da dama dai sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ba za mu yi rijista ba tun da ba kungiya ba ce — Shi'a"

Post a Comment