Nigeria: Kwastam ta kama shinakafar da aka yi da roba

Hukumar hana fasa kwauri ta Nigeria kwastam ta ce ta kama buhu 102 na wata sinkafar da aka yi da roba wacce aka shigar da ita kasar ta barauniyar hanya.
Wani babban jami'in hukumar ya ce wani dan kasuwa ne ya shigar da shinkafar domin sayarwa a lokacin bukuwan kirsimeti.
Jami'in mai kula da shiyya ta daya ta hukumar hana fasa kwauri da ke Ikeja Haruna Mamudu, yace binciken farko ya nuna cewa shinakafar ta roba tana cabewa idan an tafasa ta, sanan ya ce Allah ne kadai ya san irin illar da za ta yi wa duk wanda ya ci.
Sai dai Harun Mamudu bai bayyana yadda aka yi shinkafar ba, to sai dai ya ce sunanta "best Tomato Rice".
Ya kara da cewa ana gudanar da bincike don gano irin wannan shinkafa ta roba da ake sayarwa a kasuwa.
Wani jami'in hukumar ya shedawa BBC cewa an kama mutum daya dan Nigeria, sai dai har yanzu suna bincike don sanin daga inda aka shigar da shinkafar kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Kwastam ta kama shinakafar da aka yi da roba"

Post a Comment