Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2016

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da ya fi yin fice a bana, wato kyautar Ballon d'Or.
Ronaldo mai shekara 31, ya taimakawa Real Madrid lashe kofin zakaraun Turai a bara, ya kuma ci kwallaye uku da suka bai wa Portugal damar cin kofin nahiyar Turai a 2016.
Dan wasan na Real Madrid ya ci kyautar Ballon d'Or karo na hudu kenan, bayan 2008 da 2013 da kuma 2014.
A tarihin lashe kyauatr Lionel Messi ne ke kan gaba, wanda ya karbi guda biyar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

Related Posts :

  • Man City ta dare kan teburin Premier Manchester City ta hau kan teburin Premier, bayan da ta ci West Brom 4-0 a wasan mako na 10 da suka fafata a ranar Asabar. Sergio Aguero … ...
  • Liverpool ta samu maki uku a kan Crystal Palace Crystal Palace ta yi rashin nasara a gida a hannun Liverpool da ci 4-2 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka kara a ranar Asabar. Live… ...
  • Arsenal ta doke Sunderland 4-1 Sunderland ta yi rashin nasara a gida a hannun Arsenal da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka fafata a ranar Asabar. Arsenal … ...
  • A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La Liga wasannin mako na 10. Sai dai Cristiano Ronaldo na fama da rashin cin kwallaye a gasar ban… ...
  • Na yi shakku kan 'yan wasana - Guardiola Kocin Manchester City Pep Guardiola ya amince cewa ya nuna shakku kan 'yan wasansa ba wai kan tsarinsa na buga wasa ba bayan sun doke Wes… ...

0 Response to "Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2016"

Post a Comment