Super Falcons ta lashe kofin Afirka na bana a Kamaru

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super
Falcons, ta lashe kofin nahiyar Afirka, bayan da
ta doke ta Kamaru da ci 1-0 a karawar da suka
yi a ranar Asabar a Kamaru.
Da wannan sakamakon Nigeria wadda ke rike da
kofin, ta lashe karo na 10 jumulla a tarihi, inda ta
fara daukar kofin farko a shekarar 1991.
Wannan ne karo na hudu da Nigeria ke cin
Kamaru a wasan karshe a gasar kofin nahiyar
Afirka ta Mata.
Nigeria ta fara cin kamaru a wasan karshe 2-0 a
gasar farko a shekarar 1991 a Legas, sannan ta
doke Kamaru 4-0 a wasa na biyu a shekarar a
Yaounde.
Super Falcons ta kara doke Kamaru da ci 5-0 a
wasan karshe a shekarar 2004, sannan ta kara
samun nasara da ci 2-0 a wasan karshe a gasar
da aka yi a 2014.
Nigeria ta dauki kofin a shekarar 1991, 1995,
1998, 2000, 2002, 2004, 2006, 2010 da kuma
2014, inda Equotorial Guine ta dauka sau biyu a
shekarar 2008 da kuma 2012.
Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta mata a
shekarar 2018 a Ghana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Super Falcons ta lashe kofin Afirka na bana a Kamaru"

Post a Comment