Ronaldo da Mourinho sun kauce wa biyan haraji

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen dan wasa
Real Madrid, Cristiano Ronaldo da wasu 'yan
wasan sun zille wa biyan harajin miliyoyin daloli,
ta hanyar boye kudadensu a kasashen da ake
amfani da su don kauce wa biyan harajin.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Der
Spiegel ta kasar Jamus ya gano hakan ne ta
hanyar bayanan da aka kwarmata, cikin su har
da takardun hakika na kwangilolin da 'yan wasan
suka sanya wa hannu da bayanan sirrinsu da
kuma sakonnin imel.
Lauyoyin Ronaldo sun ce hukumomin da ke
karbar haraji na Spain sun yi bincike sosai kan
takardun harajinsa kuma ba su gano wata
badakala ba.
Sauran masu ruwa-da-tsaki a harkokin wasannin
da ake zargi da zille wa biyan harajin sun hada
da kocin Manchester United, Jose Mourinho,
wanda kamar Ronaldo, yake amfani da wani
wakili mai suna Jorge Mendes wajen ajiye
kudinsa a kasashen da ake kauce wa biyan
harajin.
Kamfanin Mr Mendes, Gestifute, ya ce Mourinho
ya cika dukkan sharudan biyan haraji na
kasashen Birtaniya da Spain.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ronaldo da Mourinho sun kauce wa biyan haraji"

Post a Comment