Sabuwar dambarwar siyasa a Gambia

adamabarrow.jpgGambia ta shiga cikin wata dambarwar siyasa, bayan shugaban kasar Yahya Jammeh ya janyen sanarwar da ya bayar a makon jiya, cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar.
Shugaba Jammeh ya ce ya na so a sake gudanar da zaben, duk da kiraye-kiraye da Tarayyar Afirka ta yi na ganin ya mika mulki cikin kwanciyar hankali.
Adama Barrow dai ya dage kan cewa shi ne ya yi nasara a zaben, sannan ya bukaci jama'ar Gambia da su yi zanga-zanga.
Duk da wannan dambarwa dai, babu wata hatsaniya a cikin unguwanni a Banjul, babban birnin Gambia.
Akasarin mutane sun yanke shawarar zama a cikin gidajensu, saboda fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali.
An ga sojoji dauke da manyan bindigogi a muhimman wurare a babban birnin kasar.
Sabon zababben shugaban kasar, Adama Barrow ya yi watsi da batun sake gudanar da sabon zabe, sannan ya yi kira ga Shugaba Jammeh da ya amince da kayen da ya sha.
Ya ce ina sanar da ku cewa, shugaba bai barin gado bai da wani iko bisa doka na yayi watsi da sakamakon zaben, da yin kiran a sake gudanar da wani. Hukumar zabe ce kadai ke da ikon shirya zabe da sanar da wanda ya yi nasara. Haka kuma akayi, ni kuma na zama zababben shugaban kasa.
Tarayyar Afirka ma ta bayyana kin amincewa da sakamakon zaben da shugaba Jammeh ya yi yanzu a matsayin abin da ba zai yiwuwa.
Ministan harkokin wajen Senegal ma ya gargadi shugaba Jammeh da kada ya yi yunkurin tauye wa jama'ar kasar 'yancin su.
'Yan kasar ta Gambia dai yanzu, sun zura ido ne suna jiran ganin abin da zai faru.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sabuwar dambarwar siyasa a Gambia"

Post a Comment