Dubban farar-hula na cikin mawuyacin hali a Aleppo

Dubban farar-hular da aka rutsa da su a Aleppo na kasar Syria na cikin mawuyacin hali a yayin da ake jan-kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati da 'yan tawaye suka kulla ta kwashe su daga birnin.
Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa sun ga mutane na kwana a cikin matsanancin sanyi ba tare da samun abinci ba.
Da alama an samu jinkirin kwashe su ne saboda jayayyar da kan fitar da farar-hular daga yankuna biyu da ke hannun gwamnati a lardin Idlib.
Sai dai gidan talabijin gwamnatin Syria ya ce motocin bas-bas sun shiga gabashin Aleppo da rana domin soma kwashe farar-hular.
Rahotanni sun ce za a kwashe mutum 1,200 a bas-bas daga yankunan 'yan tawaye yayin da za a kwashe kamar wannan adadi daga garuruwa biyu da ke hannun gwamnati a lardin na Idlib.
Motocin bas-bas din sun shiga gabashin Aleppo ne karkashin kulawar kungiyar bayar da agaji ta the International Red Cross da takwararta ta the Syrian Arab Red Cross, in ji kamfanin dillancin labarai na Sana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dubban farar-hula na cikin mawuyacin hali a Aleppo"

Post a Comment