Tinubu ya ce ba zai fita daga jam'iyyar APC ba

Fitaccen jigon nan na jam'iyyar APC a Najeriya
Bola Ahmed Tinubu ya musanta rade-radin da
ake yi cewa zai fice daga jam'iyyar.
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya wallafa a
shafinsa na Twitter cewa ya sadaukar da
rayuwarsa wajen kafa jam'iyyar don haka bai ga
dalilin fice wa daga cikinta ba.
Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da
ake rade-radin cewa ba ya jituwa da shugaban
kasar Muhammadu Buhari kuma yana shirin hada
gwiwa da wasu manyan 'yan jam'iyyar domin
kafa sabuwar jam'iyya.
Sai dai a cewar Bola Tinubu, "Wannan gwamnatin
ta APC tana son kyautata wa jama'a kuma hakan
ya fi wata bukata ta mutum daya kacal."
Ya kara da cewa "Za a yi kuskure idan ana
yunkurin kyautata wa 'yan kasa, kuma za a yi
tsare-tsare wadanda daga baya za a yi wa
kwaskwarima. Ana yin kuskure, kuma ana
gyarawa."
Shi kan sa shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari ya musanta cewa akwai takun-saka
tsakaninsa da Bola Tinubu, yana mai cewa
"Tinubu gagarabadan dan siyasa ne wanda kowa
ya san irin gagarumar gudummawar da yake
bayar wa wajen ci gaban jam'iyya mai mulki."
Masu fashin-baki a kan harkokin siyasa na cewa
Bola Tinubu bai ji dadin yadda wasu abubuwa ke
faruwa a jam'iyyar APC ba, ciki har da yadda
mutunen da yake goyon baya suka sha kaye a
zaben jihar Kogi da Ondo.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tinubu ya ce ba zai fita daga jam'iyyar APC ba"

Post a Comment