Nigeria: Buhari ya sa a binciki 'Babachir Lawal da Ibrahim Magu'

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa a binciki Sakataren gwamnatin kasar Babachir Lawal da wasu manyan jami'an gwamnati da ake zargi da aikata cin hanci da rashawa.
Mista Lawal da shugaban riko na Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC Ibrahim Magu, na daga cikin wadanda rahotanni suka ce za a bincika.
Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar, wacce ba ta ambaci sunan kowa ba, ta ce babu sani ba sabo a yaki da cin hanci da rashawar da gwamnati ke yi, kuma duk wanda aka samu da laifi ba zai tsira ba.
A makon da ya gabata ne wani rahoton majalisar dattawan kasar ya zargi Mista Lawal da bayar da kwangilar miliyoyin naira ga wani kamfaninsa.
Har ila yau an zargi kamfanin da gazawa wurin gudanar da aikin da aka bashi a wani bangare na shirin kula da 'yan gudun hijirar da Boko Haram ta fatattaka daga gidajensu.
Sai dai babban jami'in, wanda na da kusanci sosai da Shugaba Buhari, ya musanta zargin aikata ba daidai ba.
Ba ya ga Babachir, wasu rahotanni na nuna cewa har da Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, Ibrahim Magu, za a bincika.
A makon da ya gabata ne 'yan majalisar dattawa suka ki amincewa su tabbatar da shi a kan kujerarsa saboda zarginsa da sabawa ka'idojin aiki.
An zargi Mista Magu da karbar gida daga hannun wani tsohon jami'in rundunar sojin sama ta kasar, batun da ya musanta.
Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu, ya ce an umarci Ministan Shari'ar Kasar, Abubakar Malami, da ya gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ke gudana.
Tun bayan hawansa kan mulki, Shugaba Buhari ya kama manyan jami'an tsohuwar gwamnati wadanda tuni aka fara yi wa wasunsu shari'a kan zargi aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.
Masu sukar gwamnatin ta APC dai na cewa ta mayar da jami'anta shafaffu da mai, yayin da kawai take tuhumar 'yan adawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Buhari ya sa a binciki 'Babachir Lawal da Ibrahim Magu'"

Post a Comment