Ghana: Ko kun san wanene Nana Akufo- Addo?

An haifi Nana Addo Dankwa Akufo-Addo a ranar
29 ga watan Maris din 1944 a tsakiyar birnin
Accra.
Kuma gidansu ne ya zama shedkwatar jam'iyyar
siysa ta farko a Ghana wato UGCC.
Mahaifinsa da kawunsa da kakansa na daga cikin
mutane shida da ake wa kallon wadanda suka
kafa siyasa a Ghana, kuma ake muksu lakabin
Big Six, ma'ana manya shida, cikinsu har da
Kwame Nkuruma.
Nana Akufo-Addo kwararren lauya ne kuma dan
siyasa, sannan hamshakin dan kasuwa. Ya jima
yana tsayawa takarar shugagabancin kasar ta
Ghana a matakai daban-daban.
A watan Oktoban 1998, ya nemi jam'iyyarsa ta
NPP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar,
to sai dai ya sha kasa a hannun takawaransa
John Kufor, wanda ya zama shugaban kasar a
shekarar 2000
Bayan jam'iyyar ta NPP ta kafa gwamnati, Nana
Akuffo Addo ya zama babban lauyan gwamnatin
kasar kuma ministan shari'a, daga baya kuma
aka nada shi ministan harkokin kasashen waje.
To amma ya ajiye mukamin a shekarar 2007
domin tsayawa takarar shugabancin kasar.
A zaben da aka yi a ranar 7 ga watan Disambar
2008 ya samu kuri'u mafiya rinjaye a zaben
shugaban kasar, inda ya samu kaso 49 a kur'iun
da aka kada, to sai dai hakan bai sa ya samu
nasarar zama shugaban kasar ba, domin kuwa
dokokin kasar Ghana sun tanadi cewa sai dan
takara ya samu kaso hamsin sannan ya lashe
zabe.
Murnar Nana Addo da magoya bayansa ta koma
ciki a lokacin da aka je zagaye na biyu na zaben,
yayin da abokin takararsa na jam'iyyar NDC John
Atta Mills ya samu kaso 50 da 'yan kai, abinda
ya bashi damar zama shugabana kasar.
Akufo-Addo ya sake tsayawa takarar
shugabancin kasar a shekarar 2012, inda suka
gwabza da shugaba mai ci John Mahamma na
Jam'iyyar NDC.
Zaben dai ya janyo ce-ce ku-ce, daga karshe
kotun kolin kasar ta yanke hukuncin da ya raba
kan alkalanta, kuma aka tabbatarwa da
Mahamma nasara.
Tun watan Maris na shekarar 2014, ya bayyana
cewa zai tsaya takara a zaben na bana.
Don haka wannan ne karo na hudu da yake
zawarcin kujerar shugaban kasar, kuma karo na
biyu da za su fafata da abokin hamayyarsa
shugaba mai ci John Mahama.
A shekarar 2014, Nana Akufo Addo shi ne
shugaban tawagar masu sa ido a zaben
shugaban a Africa ta kudu.
A bangaren siyasa kuwa an jima ana damawa da
shi. Ya taba zama babban sakataren wata
kungiyar fautukar neman 'yanci da adalci mai
suna Peoples movement for freedom and
Justice, wacce ta jagoraci gangamin adawa da
wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka so yin
amfani da ita a lokacin, kan tsarin jam'iyya daya
a kasar Ghana.
A 1992, Nana Akuffo Addo ya zama sakataren
tsare tsare na farko na jam'iyyar NPP. A 1995
kuwa ya jagoranci wata zanga-zangar nuna
damuwa da halin matsalin tattalin arziki da aka
fuskanta a lokacin shugaba Jerry Rawlings.
An zabe shi dan majalisar wakilai sai uku daga
1996 zuwa 2008.
Ta bangaren aiki kuwa Nana Akufo Addo ya yi
aikin lauya na tsawon shekara biyar a Faransa.
Ya koma gida Ghana a 1979 inda suka hada
gwiwa wajen kafa kamfanin aikin lauya. Kuma
shi ne mutumin da ya kai wayar hannu Ghana ta
yin amfani da wata sanayya da yake da ita da
wani kamfani a Amurka.
Ta bangaren ilimi kuwa Nana Akufo-Addo ya yi
makarantar primary ta Government Boys School
ta Adabraka a Accra Gahana, Yayi karatunsa na
sikandare da kuma makarantar gaba da
sikandare a Ingila.
A shekarar 1962 Nana Addo ya koma Ghana
domin koyarwa a makarantar sikandare, inda
daga nan ya karanci tattalin arziki a jami'ar kasar
Ghana, ya kuma kammala a 1967.
Daga nan ne kuma ya koma Birtaniya inda ya
karanci aiki lauya, kuma ya zama lauya a Ingila a
1971.
Nana Addo Dankwa Akofu-Addo na da mata daya
da 'yaya mata biyar da jikoki biyar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ghana: Ko kun san wanene Nana Akufo- Addo?"

Post a Comment