'Yan wasan Najeriya mata na yajin aiki

'Yan wasan kwallon kafa mata na Najeriya Super
Falcons sun yi zaman dirshan a otal din da suke
a Abuja, sai an biya su hakkokinsu da alawus
dinsu na cin kofin da suka yi.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi wa
zakarun na Afirka da suka dauki kofin kasashen
Afirka a karo na takwas bayan sun ci Kamaru
mai masaukin baki 1-0 ranar Asabar, alkawarin
biyansu bashin kudaden da suke bi na baya kafin
a fara gasar a Kamaru.
Wasu rahotanni sun bayyana hukumar kwallon
kafa ta Najeriya ta fitar da wata sanarwar inda
ta ce babban sakatarenta Dakta Mohammed
Sanusi, ya je otal din 'yan wasan inda ya gana da
su da jami'ansu.
Sanarwar ta ruwaito Dakta Sanusin ya tabbatar
da cewa 'yan wasan da jami'ansu suna bin
kudaden, kuma ya ce ba sa farin ciki da hakan.
Amma saboda matsalar tattalin arziki da kasar
ke ciki, za su ci gaba da rarrashin 'yan wasan da
duk wadanda suke binsu kudade har lamarin ya
inganta.
Duk da rokon da hukumar kwallon kafar ta
Najeriya ta yi wa 'yan wasan su yi hakuri har
al'amura su inganta, 'yan wasan na Super
Falcons sun lashi takobin ci gaba da zaman
dirshan din a otal.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun
matsala tsakanin 'yan wasan mata na Najeriya
da hukumar kwallon ta Najeriya, NFF ba a kan
kudade.
Shekara 12 da ta wuce, 'yan wasan sun ki fita
daga otal dinsu a Afirka ta Kudu har kwana uku,
bayan da NFF din ta kasa biyansu kudadensu
bayan sun ci kofin Afirkan na 2004.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan wasan Najeriya mata na yajin aiki"

Post a Comment