Hukumar JAMB ta karo wulakanci

– Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare za ta kawo sabon salo
– Shugaban Hukumar JAMB din yace za a saka na’urar daukar hoto a dakin jarrabawa
– JAMB din za ta kawo wani tsari domin rage matsalolin da aka fuskanta a baya
Hukumar JAMB ta karo wulakanci
Hukumar JAMB ta karo wulakanci
Hukumar JAMB ta canza kidan ta don kuwa tana shirin kawo wani sabon tsari a harkar Jarrabawar Kasar. JAMB din tana shirin saka na’urororin daukar hoto na boye a dakunan zana jarrabawa.
JAMB tace daga shekara mai zuwa, duk dakin da aka ba damar daukar jarrabawa sai ya cika wannan sharadi. Hukumar JAMB tace sai an saka na’urorin daukar hoto na CCTV a dakunan Jarrabawar. Shugaban JAMB din, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka a Legas.
Farfesan yace amfanin hakan shine a ga duk abin da ke faruwa a dakin jarrabawan a ko ina a duniya. Farfesa Oloyede yace muna cikin tafiyar canji ne, don haka dole a gani a Kasa. Farfesa yace dole kuma dakin jarrabawa ya samu na’urar zana jarrabawa guda 250, da wasu kuma gudun ta-baci.
A baya dai Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare a Kasar ta rage makin da ta saka a da can na samun shiga Jami’o’in Kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hukumar JAMB ta karo wulakanci"

Post a Comment