'Yadda mijina ya so ya kashe ni saboda ba na haihuwa'

Victoria John, wata mazauniyar kauyen
Lakwushehe ce da ke Jos, a jihar Plateau a
Najeriya.
Victoria ta kasance daya daga cikin matan da
suka fuskanci musgunawa da kyama sakamakon
rashin haihuwa.
Wannan baiwar Allah dai ta hadu da mijin da ta
aura, a jami'a, a inda kuma suka yi soyayya
sannan daga bisani ta juye zuwa aure.
To amma kash! Farin cikin Victoria ya fara
gushewa ne tun lokacin da ita da angonta suka
je wurin likita kan batun haihuwa.
Mijin nata ya fara dandana mata kudarta bayan
da likitan ya sanar da shi cewa Victoria ba za ta
iya haihuwa ba.
Ga dai abin da Victoria ta shaida wa Ummulkhairi
Ibrahim a hirar da ta yi da ita:
Lokacin da Maman Philip wadda ita ce
mahaifiyar Victoria, ta ga 'yarta ta dawo gida,
hankalinta ya tashi fiye da aniya.
Ga abin da ta ce a hirarta da Ummulkhair
Ibrahim:
Wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya ta
fitar a 2004 sun nuna cewa fiye da kaso 30 cikin
100 na mata masu shekaru 25 zuwa 49, na fama
da wannan matsala.
Hukumar ta kara da cewa matan masu irin
wannan matsalar sun fi yawa a yankin Afirka da
ke kudu da Sahara.
A Najeriya kuwa kashi 10 cikin 100 na ma'aurata
ne ke fama da irin wannan matsala da Victoria
John ta fuskanta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yadda mijina ya so ya kashe ni saboda ba na haihuwa'"

Post a Comment