Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan 'yan gudun hijira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki
majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin
bayar da agaji saboda "zuzuta" halin da 'yan
gudun hijirar da Boko Hara suka kora daga
gidajensu ke ciki.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar
Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kungiyoyin
suna kambama halin da 'yan gudun hijirar ke ciki
ne da zummar samun kudi daga wajen
gwamnatoci.
Ya bayar da sanarwar ce kwanaki kadan bayan
majalisar ta dinkin duniya ta ce fiye da mutum
5m da Boko Haram ta raba da muhallansu na
fuskantar hatsarin kamuwa mummunar yunwa.
A cewar Garba Shehu, "Mun damu kwarai kan
kwan-gaba-kwan-bayan da irin wadannan
kungiyoyi ke yi game da alkaluman da suke fitar
wa kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki. Kwanan
nan wata kungiyar majalisar dinkin duniya ta ce
mutum 1000,000 za su mutu sakamakon yunwa
a shekara mai zuwa. Daga bisani kuma wata
kungiyar ta ce mutum 1m ne za su mutu."
Ya kara da cewa fitar da wadannan
mabambantan alkaluma ta nuna cewa kungiyoyin
ba su da cikakkiyar masaniya kan halin da 'yan
gudun hijirar ke ciki.
Kakakin shugaban na Najeriya ya ce gwamnati
na yin bakin kokarinta domin ganin ta sauwaka
wa 'yan gudun hijirar halin da suke ciki.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan 'yan gudun hijira"

Post a Comment