2016: Ana zaben kasar Ghana

A ranar laraba ne ake zaben shugaban kasa da
na 'yan majalisar dokokin kasar Ghana.
Shekaru 25 kenan da kasar Ghana ta koma
turbar mulkin Dimukradiyya, kuma wannan shi ne
karo na bakwai da al'umar kasar za su kada
kuri'ar zaben shugaban kasa.
A wannan zaben dai ana ganin fafatawar za ta fi
zafi tsakanin shugaba mai ci John Dramani
Mahama na jam'iyyar NDC da Nana Akufo-Addo
na jam'iyyar NPP.
Akwai kuma wasu 'yan takarar da za su wakilci
jam'iyyu hudu, da kuma indifanda.
Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-
Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar
shugabancin kasar, karo na uku kenan da yake
neman kujerar.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin cewa
idan har ya sha kaye a wannan karo, to hakan
zai kawo karshen damawa da ake yi da shi a
siyasar kasar saboda shekarunsa.
A bangare guda kuma idan har Shugaba Mahama
ya fadi zaben, to shi ne zai zamo shugaban
Ghana na farko da ya yi wa'adin mulki sau daya
a tarihin dimukradiyyar kasar.
Idan kuma ya yi nasara, zai kafa tarihin zama
shugaba na farko farar hula da ya dade ya na
mulki a kasar tun bayan da Ghana ta zamo mai
jam'iyyun siyasa daban-daban.
Saboda shi ne ya karashe sauran wa'adin mulkin
marigayi John Atta Mills da ya rasu a shekarar
2012.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "2016: Ana zaben kasar Ghana"

Post a Comment