Buhari ya musanta korar Ibrahim Magu daga aiki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya
musanta rahotannin da wasu kakafen watsa
labarai na kasar suka bayar cewa ya kori
shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa
tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC, Ibrahim
Magu daga aiki.
Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam
Garba Shehu ya fitar ranar Asabar ta ce masu
watsa irin wadannan rahotanni suna yin shaci-
fadi ne kawai.
A cewarsa, "Mun karanta rahotannin cewa an
sallami shugaban EFCC, Ibrahim Magu daga aiki.
Babu wani rohoto da babban mai shari'a na kasa,
wato Antoni Janar ya mika wa fadar shugaban
kasa a kan wannan batu. Don haka rahotannin da
ke cewa an kore shi daga aiki shaci-fadi ne
kawai".
Ibrahim Magu dai ya shiga bakin 'yan jarida sosai
tun bayan da majalisar dattawan kasar taki
amincewa ta tabbatar da shi a matsayin
shugaban EFCC, tana mai cewa ta dauki matakin
ne sakamakon wani rahoton sirri da hukumar
tsaro ta farin-kaya, DSS ta mika mata a kansa
wanda ke nuna cewa ya aikata ba daidai ba.
Sai dai masu fashin-bakin siyasa na ganin an ki
tabbatar da Mr Magu a kan mukaminsa ne
saboda takun-sakar da ake yi tsakaninsa da
shugaban DSS ba wai domin ya aikata wani laifi
ba.
A kwanakin baya ne kakakin shugaban kasar ya
ce Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga
ministan shari'ar kasar ya yi bincike kan wasu
manyan jami'an gwamnatinsa bisa zarginsu da
aikata ba daidai ba.
Kodayake bai ambaci mutanen da za a yi bincike
a kan nasu ba, amma rahotanni na cewa Ibrahim
Magu da Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir
Lawal su ne mutanen da za a yi bincike a kansu.
Shi dai Ibrahim Magu ta taka sawun manyan
mutane da dama a yakin da yake yi da cin hanci
da rashawa, cikin su har da Kanar Sambo
Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban
kasar shawara a kan sha'anin tsaro da kuma
tsofaffin manyan jami'an rundunar sojan kasar,
wadanda ake zargi da sace kudin da aka ware
domin yaki da kungiyar Boko Haram.

YOU MAY ALSO LIKE: NURA M INUWA FT ALI SHOW NEW ALBUM RUMAH

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya musanta korar Ibrahim Magu daga aiki"

Post a Comment