Ghana: 'Zan iya yin tsirara idan jam'iyyata ta lashe zabe'

Yayinda ake cigaba da kidaya kuri'ar babban
zaben kasar Ghana da aka kaɗa ranar Laraba,
magoya baya na ta tofa albarkacin bakinsu kan
inda suke ganin nasara za ta kaya.
Kowa dai na ganin jam'iyyarsa ce za ta lashe
zaben.
Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da
wasu matasa bayan kammala kada kuri'unsu.
Kuma a cikin su har da wanda yake cewa idan
dai har jam'iyyarsa ta lashe zaben to zai iya yin
tubewa tik saboda murna.
Ku saurari hirar domin jiyewa kunnuwanku:
Ana dai sa ran fitar da sakamakon zaben na
kasar Ghana ranar Asabar.
Sai dai kuma idan ba a samu dan takarar da ya
sami kuri'un da suka haura kaso 50 cikin 100 na
kuri'un da aka kada ba, to za a je zagaye na biyu
na zaben.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ghana: 'Zan iya yin tsirara idan jam'iyyata ta lashe zabe'"

Post a Comment