An wanke Didier Drogba daga zargin cin hanci

Wani bincike da aka yi kan gidauniyar da tsohon
dan wasan Chelsea Didier Drogba ke gudanarwa
ya gano cewa bai yi zamba-cikin-aminci ko cin
hanci ba sai dai watakila ya yaudari masu bayar
da agaji.
An soma binciken ne kan "wasu bayanai masu
tayar da hankali" a gidauniyar ta the Didier
Drogba Foundation a watan Afrilu.
Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da jaridar
Daily Mail report ta wallafa da ya yi zargin cewa
dan wasan ya kashe £14,115 cikin gudunmawar
£1.7m da aka bai wa gidauniyar domin yin aiki a
Afirka.
Drogba, mai shekara 38, ya bukaci jaridar ta ba
shi diyya sannan ta nemi gafararsa kan kazafin
da ta yi masa.
Sai dai hukumar da ta yi binciken ta gano cewa
dan wasan bai aikata laifi ba.
Sai dai kawai ta ce bai kamata gidauniyar ta
hada asusunta da na reshenta da ke Afirka ba.
Hakan na nufin ba a kashe kudaden da
gidauniyar ta karba a Birtaniya domin inganta
asibitoci, kamar yadda aka shaida wa masu
bayar da tallafi cewa za a yi.
Rahoton ya kara da cewa, "Masu bayar da tallafi
sun yi tsammanin za a yi amfani da kudaden da
suka bayar wajen agazawa jama'a ba ajiye su a
bankuna ba."
Kafunan da Drogba ya dauka lokacin yana
Chelsea
Kofin Premier (4): 2004-05, 2005-06, 2009-10,
2014-15
Kofin Zakarun Turai (1): 2011-12
Kofin FA (4): 2006-07, 2008-09, 2009-10,
2011-12
Kofin Lig (3): 2004-05, 2006-07, 2014-15

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An wanke Didier Drogba daga zargin cin hanci"

Post a Comment