Manyan birane hudu za su daina tuka motoci masu aiki da gas a 2025

Shugabannin manyan birane hudu na duniya sun
ce za su daina amfani da motocin da ke aiki da
gas nan da tsakiyar karni mai zuwa.
Shugabannin biranen Paris, Mexico City, Madrid
da kuma Athens sun ce za su dauki matakin ne
domin inganta iskar da mutane ke shaka.
Sun kara da cewa za su bayar da ladan kudi ga
duk mutumin da ya daina amfani da mptocin da
ke aiki da gas da kuma mutanen da suka koma
takawa a kasa ko kuma hawan keke.
Shugabannin sun bayyana hakan ne a taron da
suka yi a Mexico.
A 'yan shekarun baya bayan nan, ana ta sukar
yin amfani da motoci masu aiki da gas saboda
yadda suke gurbata muhalli.
Hukumar kula da lafiya ta duniya ta ce kusan
mutum miliyan uku ne ke mutuwa a duk shekara
sakamakon cutukan da ke da alaka da iska mai
gurbata muhalli.
Ababen hawan da ke amfani da gas suna fitar da
gurbatacciyar iskar nitrogen oxides, wacce ke yin
illa ga huhu da hanyoyin numfashi, lamarin da
kan yi sanadin mutuwar mutum.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Manyan birane hudu za su daina tuka motoci masu aiki da gas a 2025"

Post a Comment