Me ya sa 'yan Kannywood ke 'rige-rigen' kafa gidauniya?

Jaruman fina-finan Kannywood, kamar
takwarorinsu na wasu fina-finan duniya, sun
shahara wajen yin shiga irin ta ƙawa da kece
raini.
Hakan ba ya rasa nasaba da irin aikinsu da
kuma, a wasu lokutan, maƙudan kudaden da suke
samu.
Wasu majiyoyi sun shaida min cewa fitattun
jarumai - maza da mata- irin su Ali Nuhu da
Adam A Zango da Hadiza Gabo da Nafisa
Abdullahi, na samun makudan kudade ta hanyar
yin fina-finai da kuma tallace-tallace da suke yi
wa wasu kamfanoni.
Sai dai a baya, ba kasafai jaruman na Kannywood
ke fitowa fili suna nuna cewa suna tallafa wa
jama'ar da suke ciki ba.
Amma a baya bayan nan sun soma rige-rigen
kafa gidauniyoyi da zummar tallafa wa jama'a.
Daya daga cikin su, Hadiza Gabon, ta shaida wa
BBC cewa suna yin hakan ne "domin nuna godiya
ga Allah bisa baiwar da ya yi mana, sannan mu
nunawa marasa karfi cewa Allah yana tare da
su."
Ita dai wannan jaruma ta bayar da tallafi sau da
dama ga 'yan gudun hijirar da suka bar gidajensu
sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram,
wadanda yanzu haka suke sansanonin 'yan
gudun hijira.
Baya ga haka, tana taimaka wa daliban kananan
makarantu da litattafai da sauran kayan koyon
karatu.
'Marasa galihu'
Shi ma a nasa bangaren, Adam A Zango ya kafa
wata gidauniya mai suna Zango Intervention
Initiative.
A cewar jarumin, gidauniyar za ta rika bayar da
taimako ga marasa galihu da marasa lafiya da
'yan gudun hijira da marayu da zawarawa.
Zango ya ce zai samu kudin gudanar da
gidauniyar ne ta hanyar shirya bikin rawa a
dukkan jihohin Najeriya wanda zai soma a watan
Janairu mai zuwa.
'Samarwa matasa mafita'
Shi kuwa Ali Nuhu, ya shaida wa BBC cewa
kodayake bai kafa gidauniya a zahiri ba, amma
babban abin da ya sanya a gaba shi ne
taimakawa matasa domin su rika tsayawa da
kafafunsu.
A cewar jarumin, hakan zai rage matsalar rashin
aikin yin da ake fama da ita a Najeriya.
"Ni dai ba ni da gidauniya, amma ina sanya
matasa a fina-finan da nake yi domin su samu
abin da za su rika kula da kansu", in ji jarumin.
'Nuna ƙauna'
Ita ma Nafisa Abdullahi ta kafa irin wannan
gidauniya, wacce da alama take kokarin zama
yayi tsakanin jaruman.
Gidauniyar, mai suna The Love Laugh
Foundation, za ta mayar da hankali ne kan nuna
kauna da tallafi ga marasa galihu da mata da
marayu da 'yan gudun hijira.
A kwanakin baya jarumar ta shirya wani biki a
birnin Kaduna inda aka tara miliyoyin kudaden da
ta ce za ta yi amfani da su wajen tallafawa 'yan
gudun hijira da sauran mutanen da ke cikin
mawuyacin hali.
Farar-dabara
Masana abubuwan da ke faruwa a Kannywood
sun yi san-barka ga wannan kokari da jaruman ke
yi na taimaka wa al'uma.
Malam Ibrahim Sheme, wanda ya dade yana
tsokaci kan Kanyywood, ya ce matakin zai
inganta dangantakar da ke tsakanin jaruman da
al'umar da ke yi musu kallo a matsayin masu
wargaza tarbiyya.
Ya kara da cewa, "Wannan mataki yana da kyau
amma ina ganin ba shi da tsari. Ya kamata
jarumai kamar goma wadanda ke da irin wannan
aniya su hada kungiya da za ta rika aiwatar da
irin wannan shiri, ba kowa ya yi gaban kansa
ba."
"Za su iya yin amfani da kungiyar wajen neman
taimako a wurin manyan attajirai irin su Aliko
Dangote da kuma kasashen duniya.
Irin hakan ne ke faruwa a Hollywood, inda za ka
ga jarumai sun zama jakadun wasu kamfanoni ta
yadda za su rika yin amfani da matsayinsu suna
nema wa al'uma, musamman mutanen da ba su
da galihu taimako, in ji Malam Sheme.
Sai dai ya ce duk da haka abin da suke yi yana
da matukar muhimmanci wajen sauya akalar
tunanin mutanen da ke yi musu kallo irin na
masu son tozartar al'adu da dabi'un al'uma.
Wani batu kuma da masu sharhi suke zuba ido
su gani shi ne tasirin wannan yunkuri na jaruman
kan irin kallon da jama'a suke yi fagen fim din.
'Yan Kannywood dai suna fuskantar suka daga
wasu bangarorin al'umma kan cewa suna bata
tarbiyyar jama'a, abin da suka sha musantawa a
lokuta daban-daban.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Me ya sa 'yan Kannywood ke 'rige-rigen' kafa gidauniya?"

Post a Comment